Shugaba Tinubu ya dakadar da Shugaban Hukumar EFCC

Abdurrashid Bawa

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da dakatar da AbdulRasheed Bawa, shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, domin ba da damar gudanar da bincike a kan yadda ya tafiyar da shugabancin sa.

Sanarwar da Daraktan yada labarai na fadar gwamnatin tarayya Willie Bassey, yace hakan ya biyo bayan zarge-zargen cin zarafi da aka yi masa.

An umurci Bawa, da ya gaggauta mika ayyukan ofishinsa ga Daraktan Ayyuka a Hukumar, wanda zai kula da harkokin ofishin Shugaban Hukumar har sai an kammala bincike.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started