KAMAEN
-
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano tace zata cigaba da kamen mabarata.
Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano Dr Harun Muhammad Sani Ibn Sina, ya bayyana hakan a lokacin ya kewa manema Labarai karin hasken yadda dakarun Hisbah suke aikin kamen mabarata a sassan Jihar Kano. Yace zasu cigaba da kamen mabaratan sabo da gwamnatin Kano ta haramta bara a tituna da sauran guraren haduwar Jama’a.