Shugaban Kasa Bola Tinubi ya dawo gida Najeriya daga Faransa

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya koma ƙasar bayan shafe kusan mako huɗu yana ƙasashen Turai.

Tinubu ya sauka Abuja, babban birnin ƙasar ne a yau Litinin da daddare.

Cikin waɗanda suka tarbe shi akwai sakataren gwamnatin tarayya George Akume da ministan babban birnin tarayya Nyesom Wike da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.

A ranar 2 ga watan Afurilu ne Tinubu ya fice daga Najeriya zuwa Faransa inda daga can kuma ya zarce zuwa Birtaniya.

Fadar shugaban ƙasa ta ce tafiyar tasa ta aiki ne da kuma nazari kan manufofinsa gabanin cika shekara biyu da kama mulki.

Al’ummar Najeriya na kokawa kan tsadar rayuwa sanadiyyar tashin farashi da matsin tattalin arziƙi daga wasu manufofi da gwamnatin shugaban ƙasar ta bijiro da su tun bayan karaɓar mulki a watan Mayun 2023.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started