Majalisar Limaman Juma’a tace tana tare da Gwamnan Kano Abba Kabir kan bijirewa umarnin Kotun ECOWAS

Shugaban Majalisar Limaman Juma’a na Jihar Kano Sheikh Muhammad Nasir Adam, ya bukaci Limaman Juma’a dasu goyi bayan Gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf, kan kin bin umarnin Kotun ECOWAS na cewa ya soke dokar hukuncin kisa kan wanda ya yi batanci ga Annabi S. A. W.

Yace Majalisar tana goyon bayan matakin da Gwamnan Kano ya dauka Kuma tanayi masa jinjina kan tsayawa da ya yi na cewar ba zai soke dokar kisa kan duk Wanda yayi batanci ga Annabi Muhammadu S.A.W ba..

Sheikh Muhammad Nasir Adam, kin yin biyayya ga Umar Kotun ECOWAS ya nuna cewa Gwamnan Kano Yana nuna cewa Manzon Allah S. A. W. a cikin zuciyarsa..

Shugaban Majalisar Limaman Juma’a yace dukkan Musulmi akan wannan fahimtar suke duk Wanda ya yi zagi ko taba martabar Annabi Muhammadu S. A. W hukuncinsa kisane..

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started