Gidauniyar Alhuda ta rabawa Marayu da Marassa karfi su 67 kayan Sallah

Rabon Tallafin kayan Sallah na Marayu, da Marasa karfi. Maza da Mata, Yara a Adadin Mutum 67 suka amfani a Karo (7) a karkashin jagorancin kungiyar Alhuda Foundation Dorayi.5

Tallafawa marayu a watan Ramadan da bayansa Yana Kara kusanta mumini ga Allah mahalicci.

Dattawan unguwar Dorayi kanfako sun bayyana hakan ne a wajen rabon kayan Sallah ga Marayu Maza da mata da Marassa karfi da Mahaifansu.

Sunce marayu da Mahaifansu mata Suna cikin halin bukatar tallafi, Dan haka suka taimakamusu da kayan sawa na Maza da mata domin rage musu radadin rashin Mahaifansu.

Mazauna unguwar Dorayi kanfako sun yabawa Gidauniyar Alhuda bisa farincikin data sanyasu..

Wannnan shine karo na bakwai da Gidauniyar Alhuda take tallafawa Marassa karfi dake unguwar Dorayi kanfako a cikin Birnin Kano.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started