A Ranar 18 ga watan Disamba 1980 rikicin Maitatsine ya barke a Kano

A Rana Mai Kamar Ta Yau 18 Ga Watan Disamba 1980 Aka Soma Yakin Maitatsine A Birnin Kano.

A Zamanin Gwamnan Kano Alhaji Abubakar Rimi Da Shugaban Kasa Alhaji Shehu Aliyu Shagari.

Rikicin da makamin da akayi kwana 10 ana fafatawa ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 10,000, ciki har da yan sanda 100 da kimanin sojoji 35 har da shi kansa Muhammadu Marwa (Maitatsine).

Makasudin rikicin Maitatsine ya faru ne a unguwar yan awaki. Yan awaki unguwa ce daga gabas, ta yi iyaka da unguwar Fagge wacce ta ke da mashahuran mutane masu arziki, malamai da ’yan kasuwa da sauransu, misali a bangaren masu arziki akwai irinsu Alhaji Garba A.D. Inuwa, da Alhaji Sama’ila maiguza.

A cewar labarin da ta buga a shekara ta 2010 jaridar Sunday tace Sojojin Najeriya sun kona gawar Maitatsine, wanda yanzu haka yana cikin kwalbar da aka ajiye a dakin gwaje-gwaje na ‘yan sanda a Kano.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started