
Shafin TikTok ya ce ya goge bidiyoyi sama da miliyan 2.1 a Najeriya a cikin wata shida na farkon 2024 saboda saɓa ƙa’idojinsu.
Kamar yadda rahoton tabbatar da bin dokokin amfani kafar da aka kamfanin ya fitar a ranar Talata ya nuna, kamfanin ya ce ya ɗauki matakin ne a cikin ƙoƙarin da yake yi na tabbatar da samar da daidaito da kuma tsabtace kafar.
“Bincike ya nuna cewa kashi 99.1 na bidiyoyin nan an cire su ne tun kafin a kawo ƙarar su, sannan kashi 90.7 an cire su ne a cikin awa 24. Waɗannan alƙaluman suna tabbatar da ƙoƙarin kamfanin TikTok na hana yaɗa abubuwa marasa kyau, domin tabbatar da samar da kafa mai kyau ga ma’abota kafar a Najeriya,” kamar yadda rahoton ya nuna.
Sai dai waɗannan bidiyoyin da aka goge ba su ma kai kashi ɗaya cikin ɗari ba na bidiyoyin da ƴan Najeriya suka ɗora a zamanin watannin da aka yi nazari domin wannan rahoton.
A duniya, TikTok ta ce ta cire sama da bidiyoyi miliyan 178 a watan Yunin 2024, inda ta ce bidiyoyi miliyan 144 daga ciki kwamfuta ce ta goge su.Aika, TikTok ya goge bidiyo miliyan 2.1 a Najeriya
Leave a comment