Kungiyar Iyaye da Dalibai P. T. A reshen Jihar Kano tayi kukan rashin biyan kudin tallafi daga iyaye

Kungiyar iyaye da dalibai ta P.T.A ta kasa reshen jihar Kano, ta koka game da yadda Iyayen yara basa iya biyawa ya’yan su kuɗin PTA a ƙarshen zangon karatu.

Shugaba kungiyar na jiha Alh. Sani Salisu danhassan ne ya bayyana hakan a yayin ziyarar wasu daga cikin makarantu dake jihar nan.

Alh Salisu danhassan yace kungiyar PTA kungiya ce mai zaman kanta kuma kowace kasa a duniya akwai ta babban aikin ta kuma shine taimakawa harkar koyo da koyarwa ga dalibai.

Yace dole sai Iyaye sun taimakawa yunkurin gwamnati wajen bada Naira ɗari zuwa ɗari biyu domin kananan ayyuka a makarantu.

Daga na sai yai kira ga malamai da suji tsoron Allah Wajen amfani da kudaden ta hanyar da tadace .

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started