


An bukaci al’ummar Musulmi kan cigaba gaba koyi da hallayen Annabi (S.A.W).
Bayanin hakan ya fito ta bakin Alh Baba Habu Mika’ilu Warure, yayin taron Mauludi tunawa da ranar haihuwar annabi (s a w ) wanda ya gudanar a kofar gidansa Anan birnin Kano
Maulidin da Kara Fara shi karon farko da iyalansa da yan uwansa suka shirya Don nuna farin cikinsu da murnar ranar haihuwar Ma’aiki annabi (s a w)
Da yake jawabinsa Alh Baba Habu Mika’ilu Warure ya kuma Shawarchi Al’ummar wajan cigaba da koyi da dabi’un Annabin Raham, inda ya kara da kira ga mawadata wajan taimakawa Al’umma musanman kan halin Tsadar rayuwa da ake ciki da taikamawa marasa lafiya a asibitoci da unguwani
Baba habu, ya sake jan hankalin jama’ar jihar Kano da su cigaban da gudanar da addu’ar samun cigaban zaman lafiya Mai dorewa a Jihar Kano tare da cigaban da baiwa jami’an tsaro gudun mawa wajan tabbatar da tsaro
Leave a comment