JAGORAN MATASAN BICHI YA JAGORANCI RABAWA DATTAWA SAMA DA DARI BIYAR NAIRA DUBU 20K

JAGORAN MATASAN KARAMAR HUKUMAR BICHI HON. ALH. MUSTAPHA KABIR ABUBAKAR (JAGORA) YA JAGORANCI BAWA DATTAWAN KARAMAR HUKUMAR BICHI KIMANIN SAMA DA MUTUM DARI BIYAR (500) TALLAFIN NAIRA DUBU ASHIRIN KOWANNENSU (#20,000).

Jagoran Matasa Karamar Hukumar Bichi Alh. Mustapha Kabir Abubakar (Jagora) ya Jagoranci bayarda tallafin ne a ranar Asabar ga Iyaye Dattawa sama da Mutum Dari Biyar (500) Wanda kowannensu ya rabauta da Naira Dubu Ashirin – Ashirin (#20,000).

Kamar Yadda aka sani wannan shine Karo na Hudu inda Jagoran yake jagorantar bada wannan tallafi Wanda Matasa da Dattawan suke amfani da wannan kabakin Arziki.

A yayin wannan taro Jagoran Matasan yayiwa Zunzurutun Daukakin Matasan Karamar Hukumar Bichi Allurar cewa kowa ya zamo cikin shirin jin Kiran Jagoran domin suma suzo su anshi nasu tallafin kamar Yadda ya Saba daga nan zuwa kowane lokaci.


A yayin taron an gudanar da Addu’oi na musamman ga Maigirma Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Karamar Hukumar Bichi a Zauren Majalisa Wanda kuma shine Shugaban Kwamitin Kudi da Tsare – Tsare na Majalisar Tarayya Najeriya wato Hon. Engr. Abubakar Kabir Abubakar Bichi FoE.


Taron ya samu Halartar, PA Zaharaddeen Kabiru Hon Muktar Bagudu, Alh Gambo Tinki, Hon. Muhammad Ado, Alh. Bello Kabir Baban Hajiya, Alh. Murtala Namowa, SLA. Abubakar Aminu Ibrahim Hon Usman Nanaba Da sauran Ma’aikatan Maigirma Danmajalisar tarayya.

SLA. Aliyu Abdullahi Habibu
A Madadin SLA’s Forum.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started