Hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Kano ta sakawa Hukumar NAHCON sama da biliyan 18, domin Hajj bana.

Babban Daraktan Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Alh Lamin Rabi’u Danbappa yace  hukumar ta aikawa Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) sama da Naira biliyan 18 domin shirye-shiryen aikin hajjin shekarar 2024.

Yace  duk da cewa mutane 3,110 sun biya kuɗin aikin hajjinsu, yawancinsu suna jiran bizarsu daga Hukumar NAHCON.

Danbappa ya kuma buƙaci hukumar da ta hanzarta bayar da bizar kafi ranar da za a rufe yin bizar.

Ya jaddada ƙudirin Gwamnatin Kano na kammala gyara sansanin alhazai kafin a fara jigilar maniyyata.

Laminu Danbappa, ya ƙara da cewa, “ba kamar shekarar da ta gabata ba, a  wannan shekarar gwamnati ta samar da dukkan kayayyakin da ake buƙata a sansanin alhazai gabanin gudanar da aikin Hajji domin amfanin maniyyata.

Da take jawabi, Hajiya Rabi  Hadiru Nyako Jami’ar gudanarwa a ofishin NAHCON da ke Kano, ta bayyana ƙudurinta na magance ƙorafe-ƙorafen biza.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started