Halartar miniyata aikin hajj cibiyoyin gwajin lafiya yana da alfanu a garesu-DG Laminu Danbappa


Darakta Janar na Hukumar Alh Laminu Rabi’u Danbappa, ya bayyana hakan a lokacin rangadin duba yadda aikin yake tafiya a sansanin Alhazai, ya himmatu wajen ganin Maniyatan Jihar Nan suna cike da koshin lafiya.

Hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Kano ta jaddada muhimmancin zuwa wajen gwajin duba lafiyar maniyata da ake gudanar yanzu haka ga dukkan alhazan Jihar Kano.

Ya kuma bukaci daukacin Maniyatan dasu ziyarci guraren duba lafiyar su domin yi musu gwaje-gwaje dan ganin sun gudanar da aikin Hajj cikin kuzari.

Yana Mai cewa “mun baiwa kula da lafiyar maniyatan Jihar nan fifiko, tare da halartar cibiyar tantance lafiyarsu dake gudana yanzu haka”, Ya Kuma bukaci hadin hakan dukan maniyatan dasu baiwa   Jami’an lafiya hadin Kai domin ganin sun gudanar da aikin su yadda ya kamata.

Anata bangaren Hajiya Binta Yusuf, Jami’ar da
ke kula da sashin lafiya na Hukumar Alhazai ya Jihar Kano, ta jaddada muhimmancin aikin , da kuma gudunmawar da yake baiwa Maniyata, domin ganin sun gudanar da aikin hajj ci ki in koshin lafiya.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started