
Babban Daraktan Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa, ya yi alkawarin hada kai da ma’aikatar kula da harkokin addinai ta jiha.
Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya bayyana haka a yau a lokacin da ya karbi bakuncin kwamishinan ma’aikatar harkokin addinai a ofishin sa.
Danbappa, ya yaba da irin gagarumar gudunmawar da ma’aikatar ta bayar a lokacin gudanar da aikin Hajjin bara, ya kuma nuna jin dadinsa da tallafin da suka ba su.
Ya kuma Sha alwashin bai wa kwamishinan hukumar cikakken hadin kai domin cimma burin da ya sanya agaba , inda ya bayyana ziyarar a matsayin wacce ta dace.
A nasa jawabin kwamishinan ma’aikatar harkokin addinai na Jihar Kano Hon Sheikh Ahmad Tijjani Auwal ya jaddada muhimmancin samar da kyakyawar alaka tsakanin ma’aikatar da hukumar alhazai.
Sheikh Ahmad Tijjani ya ci gaba da bayyana kudirin ma’aikatar na yin aiki kafada da kafada da hukumar jin dadin alhazai ta jiha, tare da rawar da take takawa a harkokin addinai a jihar Kano.
A karshe ya mika godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki bisa jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma tallafin aikin Hajji daya baiwa maniyyatan da suka yi rajista a jihar Kano.
Leave a comment