
Rundunar yansandan Jihar Kano zata samar da ofishin Jami’an Anti-Daba a unguwar Dorayi da kewaye.
Masu Mai unguwanni dake Dorayi da kewayenta sun amince da cewa dole kowa ya Fito ya bada gudunmowar sa.
Kwamishinan Yansanda na Jihar Kano ya shale a kawo Jami’an yansanda na Anti-Daba da Anti-roberry Squad a Yankin Dorayi.
Kazalika duk Wani Mai Daukar makami ya Fito kwace a Matsayin Dan Fashi kamar yadda doka ta fada.
Yanzu haka rundunar yansandan ta ayyana neman Mutane (35) mazauna Dorayi da kewaye dasu kawo Kansu gaban fishin Yansanda mafi kusa dasu.
” Duk Wanda aka kama Yana kokarin tada zaune tsaye kuma mahaifinshi ya zo don Karbar sa a hannun Yansanda to a hado da mahaifin zuwa Shalkwatar Yansanda”.
Kwamishinan yayi gargadi ga iyaye dasu Kara kulawa da yayansu domin bazai dagawa kowa Kafa ba.
Leave a comment