Taimakawa Marayu da Marassa karfi zai kawo ƙarshen Talauci da tsadar rayuwa-Alhuda

Tallafawa marayu da marassa karfi da ke cikin Al’umma zai kawo saukin yunwa da Talauci da Jama’a suke fama dashi.

Shugaban Gidauniyar  Al, Huda dake unguwar Dorayi fako Ali Abdullahi, ya bayyana hakan a lokacin da ya Jagorancin rabon kayan Sallah ga Marayu 80 a yau Lahadi.

Yace ganin halin da Jama’a suke ciki hakan yasa suka tallafa musu, sama da yadda sukai a bara.

Ali Abdullahi, yayi kira ga madawata da dai dai kun  Jama’a dasu cigaba da taimakon marayu da sauran marassa karfi.

Alh Mustapha Kasim Shugaban Kwamitin dattinai na unguwar Dorayi fako, yace suna suna bayar da tallafi ga kowane bangare musamman lafiya da tsaro da lantarki.

Wakilin mu Abubakar Sale Yakub, ya rawaitomana  cewa wata uwar marayu kuma Yar gudun hijira tace taji dadi so sai ga wannan tallafin kayan Sallah da aka baiwa ‘ya ‘yanta.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started