Kotun tafi da gidanka me kula da sha’anin Alhazai ta Jihar Kano ta mika rahoton aikin hajji bara.

Daga- Abubakar Sale Yakub

Mai rikon Shugabancin Kotun Alh Mustapha Datti Sa’ad ya gabatar da kundin bayanan ga Babban Daraktan Hukumar alhazai na Jihar Kano Alh Laminu Rabi’u Danbappa, a ranar Juma’a.

Rahoton ya kumshi dukkan bayanan abubuwa da suka faru ciki harda kalubale da nasarar da aka samu.

A Hajj bana Kotun tafi da gidanka ta alhazai ta samu sahalewa daga Gwamnatin Kano wajen fara shirye shiryenta na Hajj bana.

Wannnan Yana cikin kokarin Kotun ta ganin an gudanar da aikin Hajj cikin nasara

Da yake mayar da jawabin Darakta Janar na Hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Kano Alh Laminu Rabi’u Danbappa, ya bayar da tabbacin mikawa mataimakin Gwamnan Kano bukatun da suka nema, Wanda shine Shugaban da ake kula da dukkan sha’anin da ya shafi  Hukumar.

Ya Kuma bayyana muhimmacin da lokaci da yin aiki tare dan bukatun alhazai.

Sanarwar da Jami’an Hulda da Jama’a na Hukumar Sulaiman Abdullahi Dederi ya fitar tace Alh  Laminu Rabi’u yace cigaba da cewa akwai alakar aiki tare tsakanin Kotun tafi da gidanka da Hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Kano wajen tabbatar da cewa an samu nasara kamt yadda Gwamnatin Kano ta himmatu a lokacin aikin Hajj, da Kuma ganin an gudanar dashi lafiya.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started