
Daga Abubakar Sale Yakub
Mai kwacen wayan nan da mota ta buge shi a Kano ya rigamu gidan gaskiya , a cewar rundunar ’yan sandan jihar Kano.
A safiyar ranar Talata ce mai kwacen wayan ya ce ga garinku nan a inda aka kwantar da shi, a Asibitin Murtala, inji kakakin rundunar, Abdullahi Harun Kiyawa, ya sanar.
GASKIYATA ta ruwaito cewa a ranar Lahadi mota ta buge mai kwacen wayar lokacin da yake kokarin tserewa bayan ya yi wa wata mata fashin wayarta a Titin gidan zoo.
Kakakin ’yan sandan jihar Kano, Haruna Abdullahi Kiyawa, ya ce mota ta kade shi ne a yayin da yake kokarin tsallaka titi bayan ya yi fashin.
Leave a comment