An samu raguwar masu Shan Taba Sigari a Duniya

Daga Abubakar Sale Yakub

An samu raguwar masu shan taba sigari daga mutum guda cikin kowanne uku zuwa mutum daya cikin kowanne biyar a duniya, a cewar hukumar lafiya ta duniya.

Hakan na kunshe ne a wani rahoto da hukumar ta fitar a ranar Talata.

Rahoton shi ne na baya-bayan nan da ya yi nazari a kan shan taba a shekarar 2022.

WHO ta ce fiye da mutane miliyan bakwai ne ke mutuwa duk shekara a duniya sakamakon shan taba sigari.

Inda a ciki hukumar lafiyar ta yi kiyasin cewa sama da mutum biliyan daya da miliyan 200 ne ke shan taba a duniya.

Rahoton ya nuna cewa kasashe 150 na duniya sun samu nasarar rage masu shan taba, inda kasar Brazil da Netherlands ke kan gaba.

Nasarar da ta alakanta da aiwatar da manufofin da ke dakile shan sigari, duk da yukurin da kamfanonin sigarin ke yi na kawo nakasu.

Rahoton ya kuma ce kudu-maso-gabashin Asiya shi ne kan gaba da 26.5% na masu shan sigari a duniya.

Sai nahiyar Turai da ke biye da ita da kashi 25.3%.

Amma rahoton ya nuna cewa mata masu shan tabar yawansu ya ninka ne a nahiyar Turai.

Haka kuma ba a samu wani sauyin azo a gani ba dangane da raguwar masu zukar taba sigari a wasu kasashen duniya tun 2010.

Yayin da kasashe shida kuma karuwa masu shan tabar suka yi, wato a Congo, Egypt, Indonesia, Jordan, Oman, da jamhuriyyar Moldova.

Masana kiwon lafiya sun ce shan taba sigari na janyo wasu manyan cututtuka da suka hada da cutar sankara ko kansa, ciwon zuciya, ciwon huhu da sauransu

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started