


Daga Abubakar Sale Yakub
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa, Darakta Janar, ta dukufa wajen samar da ingantattun masaukai ga maniyyatan Jihar Kano a kasar Saudiyya.
A sanarwar da Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace a ranar Laraba ne Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa tare da hadin gwiwar hukumar alhazai ta kasa NAHCON suka sanya ido kan yadda za’a zabo masaukai a kasar Saudiyya.
Manufar hakan ita ce tabbatar da cewa maniyyatan aikin Hajin bana na Jihar Kano ba su gamu da wahala ba a lokacin tafiya kasa mai Tsareki domin gabatar da aikin Hajji.
Yunkurin hadin gwiwa na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano da Hukumar Alhazai ta kasa, ya mayar da hankali ne wajen ganin an samar da gidajen da suka dace ga maniyyatan Jihar Kano.
Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya jaddada kudirin hukumar na samar da yanayi mai kyau da jindadi ga daukacin alhazan Jihar Kano domin su samu nutsuwar mayar da hankalinsu kan ibadar aikin hajji.
Shirin na Hadin gwiwane tsakanin hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano da hukumar alhazai ta kasa, ya kuma jaddada kula da dukkan mahajjatan sannan zasu samu gamsuwa.i daya ga maniyyatan jihar Kano baki daya.
Leave a comment