Hukumar kula da Asibitocin Jihar Kano ta dakatar da wasu Ma’aikatan Asibitin Imamu Wali

Daga Abubakar Sale Yakub


Sakataren zartarwa na hukumar kula da asibitocin jihar Kano Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya amince da dakatar da jami’an tsaron asibitin haihuwa na Imamu Wali sannan ya umarci zone, wato shiya  da ta kawo wasu jami’an tsaro tare da sanya su cikin gaggawa.

Wannan ci gaban ya biyo bayan wani faifan bidiyo na wata mata mai nakuda wadda daga baya ta haihu a cikin motar sakamakon sakacin da jami’an tsaron asibitin.

A cikin faifan bidiyon da ya yadu, za a iya ganin mijin matar ya yi ta kwankwasa Kofar Asibitin ba kakkautawa amma jami’an tsaro ba a gano inda suke ba, wanda hakan ya sa mijin ya dauki hoton bidiyon hakan yasa  lamarin ya ci gaba da yaduwa.

Dr. Nagoda,  ya bayyana cewa,  lamari ya faru ne a ranar 26 ga watan Nuwamba, inda wata mata kuma tana nakuda, kuma jami’an tsaro ba sa bakin Kofa   domin mai juna biyun ta samu damar shiga  Asibitin da wuri, don haka sai mijin ya garzaya da ita asibitin kwararru na Murtala Muhammad. wanda shine mafi kusanci.

Hakazalika Dr. Nagoda ya amince da dakatar da Jami’an dakin gwajegwaje su uku nan take wadanda aka sakaya sunayensu,  saboda laifukan da suka hada da sakaci, karbar kudi da kuma ayyukan jima’i  da marassa lafiya da ba za su iya biyan kudin asibiti ba.

Ya bayyana cewa dakatarwar ta su ya zama dole kuma za a kafa kwamitin da zai gudanar da bincike, bin hanyoyin da suka dace, tare da  basu  wasikar amsa tambaya, ya kara da cewa  duk kansu an  dakatar su.

Sakataren zartarwa ya ci gaba da bayanin cewa jama’a da ma’aikatan Hukumar kula da Asibitoci n Jihar Kano,  ya kamata su sani cewa “muna da tsarin tsaro na cikin gida don tantance kwarewar mu a asibiti, sadarwa da kuma da’a ga kwararru.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started