Karancin takardar Naira ta yi kamari a birnin Abuja

Wasu sassa na babban birnin tarayya, FCT, sun fara fuskantar karancin kudin Naira, a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke fara bukukuwan Kirsimeti.

A kalla bankunan kasuwanci guda bakwai a unguwar AYA da ke Abuja sun kasa raba kudi a ranar Alhamis.

Wakilin DAILY POST, wanda ya ziyarci wadannan na’urorin ATM a yammacin ranar Alhamis, ya ruwaito cewa bai iya janyewa ba, kuma kusan mako guda kenan lamarin.

Wakilinmu, ya lura cewa, masu POS, sun yi layi a  bankunan domin samun kudade dan gudanar da sana’ar su .

Daya daga cikin masu sana’ar  POS, wanda ya bayyana kansa a matsayin Samuel, ya koka da yadda na’urorin ATM din ba sa raba kudi kamar yadda ake tsammani.

“Tun da muka shiga watan Disamba wadannan na’urorin ATM din basa bayar da kudi so sai.

“Akwai karanci naira kuma mai yiyuwa ne saboda muna cikin  watan Disamba, amma CBN ne kadai zai iya bayyana wannan sabon karancin,” inji shi.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Babban Bankin Najeriya CBN ya ba da umarnin cewa duka tsofaffin takardun   Naira za a cigaba da amfani dasu  bisa doka a Najeriya.

Kotun koli  a hukuncin da ta yanke ta amince da bukatar  gwamnatin tarayya  ta neman ta  dage wa’adin ranar 31 ga watan Disamba kan amfani da kudi N200, N500, da N1,000.

Yayin da yake mayar da martani kan hukuncin, CBN ya ce: “Don kauce wa shakku, Kotun Koli ta ba da umarnin cewa tsofaffin takardun kudi na N200, N500 da N1000, tare da sake fasalin su, za su ci gaba da zama doka.

“Saboda haka, bisa ga sashe na 20 (5) na dokar CBN ta shekarar 2007, duk takardun kudi da babban bankin Najeriya ya fitar za su ci gaba da zama a kan doka har abada.”

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started