Daga Abubakar Sale Yakub
Hukumar Kula da Zirga zirgar Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta bayar da wa’adin awa Arba’in da hudu (44) ga masu kasa Kaya su daina kasuwanci kan gadar Kurna Babban Layi da Gadar Kurna Yandoma.

Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka a yau, lokacin da ya tura tawagar jami’an Hukumar KAROTA a karkashin jagorancin Daraktan Ayyuka na Musamman Malam Tasiu Gambo domin ganin halin da gadojin suke ciki, tare da bayar da umarnin tashi daga wannan wuri.

Hukumar ta umarce su da su gaggauta tashi a daga wannan guri domin kuwa, ba a yi gadar domin a kasa kaya ba
A jawabansu daban daban shuwagabannin wajen sun bayar da tabbacin yin biyayya ga umarnin gwamnati kafin cikar wa’adin da aka saka musu
Alummar unguwannin ne suka yi korafi dangane da kasuwancin da ake yi a kan gadojin.

Haka kuma tawagar Hukumar ta karasa kasuwar Rimi, ta umarci masu kasa kaya a kan titi da su daina kafin Hukumar ta dauki matakin kwashe kayan.
Leave a comment