Allah Sarki Al’ummar Kauyen Tudun Biri an kashesu bada hakkin su ba

Yarinyar data tsira

Hawaye Yana cigaba da zuba a fuskar Mai tausayi al’ummar Kauyen Tudun Biri sun mutu bada hakkinsu ba.

cikin shekaru 20 da suka gabata yankin arewacin Najeriya Yana zaune lafiya batare da samun tashin hankali na daukar makamai daga wasu mutane ba.
Sai dai akan samu fadace fadacen kabilanci a wasu Yan kunan .

A yanzu kuwa Arewacin Najeriya cike yake da matsaloli iri daban daban , tsaro, Talauci rashin, ingantatcen ilimi.
sabanin yankin kudancin Najeriya, abin takaici shine yadda rundunar sojan kasa ta Najeriya ta cillawa mutanen da suke gudanar da taron Mauludi bama bamai a kauyen Tudun Biri a Jihar Kaduna.


hakan ya haifar da mutuwar Yara da Mata da Tsofaffi da jikkata wasu mutane da dama har yanzu ba a iya tantance ainihin mutane nawa ne suka rasu ba.


Rundunar sojan Najeriya ta kanta tace kuskurene Amma fa wannnan bashinw na farko ba a ya taba faruwa a Jihohin KATSINA da Zamfara da Niger da Sokoto.

Shin wane mataki Gwamnatin Tarayya zata dauka kan wannan ganganci?

Shin Jagororin Arewa wane mataki zasu dauka?

“Tawagar Gwamnatin Tarayya bisa Jagororancin mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima yace akwai Shirin Fulaku na kula da Yan gudun Hijira Al’ummar kauyen Tudun Biri sune zasu fara cin gajiyarsa. “

Yanzu Yan Najeriya musamman yankin Arewa sun zuba Ido suga aikin bincike da bayar da rahoto da kwmaitin da gwamnati ta kafa zai bayar, da kuma irin matakin da za a dauka domin kaucewa irin wannnan sakaci a nan gaba.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started