
Rundunar Yan sandan Jihar Kano ta Bayar da Umarnin Kamo Dan Sandan da ya harbe wani Matashi har lahira a Unguwar Kurna dake karamar Hukumar Fagge.
Ha Kuma Kwamishinan yace za’ayi Bincike akan jami’in Dan sandan da laifin kisan Kai da makami
Kwamishinan Yan sandan Jihar Kano CP Muhammad Hussain Gumel ta Cikin wata Sanarwa da Kakakin Rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya Fitar Yace
Tuni Kwamishinan ya umarci Babban Baturen Yan sanda Dake kula da shiyyar Dala ( Area Commander) ACP Nuhu Mohammed Digi da ya Gudanar da Bincike akan Dan Sandan da Ake zargin yayi Harbi har yakai ga Hallaka Matashin
Kwamishinan yace Bayan kammala Bincike za ayi adalci tare da Hukunta Wanda Ake Zargi da Yin Harbin ba’bisa Ka’ida ba.
Ya Kuma Mika sakon ta’aziyya ga Yan uwa da Abokan arzikin mamacin tare da kira ga al’ummar Yankin su kasance Masu Bin Doka da oda.
Jiya ne dai Ake zargin jami’an Yan sanda da Harbin wl Matashin Mai suna salisu Player da wasu mutane Biyu.
Majiyarmu ta ziyarci gidansu mamacin Kuma Wani Dan uwansa Mai suna Muktar Kabiru ya ce suna Neman Hakkin Dan uwansu da jami’an Yan Sandan suka hallaka
Leave a comment