



Daga_Abubakar Sale Yakub
Tallafawa fannin Kula da lafiyar Al’umma babban aiki ne dake kan gwamnati da mawadata da kungiyoyi da sauran Jama’a.
Hakan yasa Manajan Daraktan Kasuwar Kantin Kawari Alh Hamisu Sa’ad Dohon Nama, ya bijiro da Shirin kula da lafiyar Jama’a da basu Magani kyauta ga Al’ummar mazabu 12 a karamar Hukumar Dala a cikin birnin Kano.
Alhaji Ibrahim Garba Kamfani (Mataimaki na Musamman ga Mai Girma Gwamnan Jahar Kano a Kasuwar Kantin Kwari kuma shugaban Sashen Kasuwancin Masarautun Arewa) ya Wakilci Mai Girma MD na Kasuwar Kantin Kwari Alhaji Hamisu Sa’ad Dogon Nama a wajen taron bayarda magunguna kyauta ga marasa lafiya wanda aka shiryashi don al’ummar Mazabu 12 na Karamar Hukumar Dala.
Alhaji Hamisu Sa’ad Dogon Nama, yace daukar nauyin shirin da aka fara gudanarwa a Mazabar Dala zai taimakawa Al’umma marassa karfi wajen samun Magani kamar yadda Gwamnatin Kano takeyi.
Ya cigaba da cewa sannu ahankali za’a ziyarci sauran Mazabun 11.
Leave a comment