
Daga Abubakar Sale Yakubu
Darakta Janar na Hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Kano Alh Laminu Rabi’u Danpappa, ya fitar da sanarwar a yau a karamar Hukumar Gaya.
Alh Danpappa yace yace rasuwar Alhajin Jihar Kano, Wanda ya rage a kasar Saudia.Alh. Umar Hamza ta bigi zuciyarasa.
Alh Hamza Umar, Yana da shekaru 75, ya rasu ranar Alhamis bayan fama da rashin Lafiya, mahukuntan Asibitin Kasar Saudiya suka tabbatar da rasuwarsa.
Darakta Janar na Hukumar jin dadin alhazan, ya bayyana jimamk na rashin Alh Umar Hamza, wanda ya bayyana a matsayin malamin Addinin Isalam ya kuma yiwa iyalansa ta’aziyya bisa rashin mahaifinsu da sukai.
Alh Laminu Rabi’u Danpappa, amadadin Hukumar gudanarwa ta Hukumar jin dadin alhazan Jihar Kano ta mika sakon Gaisuwa ga Jafar Umar Hamza, Dan marigari da ilahirin Yan uwa da mokata da Al’ummar Musulmi baki daya .
Sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar jin dadin alhazan Jihar Kano Sulaiman Abdullahi Dederi, ya fitar ta e Alh Laminu Rabi’u, yayi Addu’ar Allah ya jikan mama cin yasa Aljannace makoma Ameen.
Leave a comment