
Sanannan Malamin Addinin Musulunci na Jihar Kano, Sheikh Yusuf Ali (Sarkin Malaman Gaya), ya rasu yana da shekaru 73 a daren ranar Lahadi.
Sanarwar rasuwar fitatcen Malamin ta fito ne ta hannun dansa Muslihu Yusuf Ali ta kafar sadarwasa ta Facebook a daren ranar Lahadi.
An haifi Sheikh Yusuf Ali a shekarar 1950, a garin Gaya da ke Jihar Kano.
Yayi karatuttuka a fannonin addinin Islama da Sharia, ya zama ma’aikacin kotun Shariar Musulunci a shekarar 1974, Wanda ya kai matsayin Rajistara (magatarda)a babbar kotun Shariar Musulunci, Ya kuma zama darakta a wannan kotun.
Sheikh Yusuf Ali ya yi ritaya daga aiki a shekarar 2009. Ya kuma ci gaba da koyarwa da yada da’awa da kuma samar da magunguna ga marasa lafiya musamman masu shafar aljannu.
Za a yi jana’izarsa a yau Litinin a Masallacin Murtala da ke unguwar Hausawa da ke kan titin zuwa gidan namun daji da karfe 1:30 na rana.
Leave a comment