Gwamnatin Kano tace ta gamsu da yadda Jami’an kashe gobara suke aikin su a Kasuwar Kantin Kwari—SA Ibrahim Company

Daga Abubakar Sale Yakub

Alhaji Ibrahim Garba Kamfani (Mataimaki na Musamman ga Zababben Gwamnan Jahar Kano, His Excellency Engr. Abba Kabir Yusuf, a Kasuwar Kantin Kwari) ya bayyana hakan a lokacin ziyarar aiki da ya Kai ofishin Hukumar Kashe gobarar na Jihar Kano da ke a cikin kasuwar.

Yace ya ziyarci ofishin Hukumar Kashe Gobara (Yan Kwana-Kwana) ta Kasuwar Kantin Kwari domin duba ayyukansu, da kuma daukar bayanai gameda matsalolinda suke fuskanta don daukar matakai na musamman da zasu saukakawa aikinsu.

Cikin matakan harda samarda wajen ajje ababen hawansu don kawardasu daga kan titi.

Tareda bawa mai Gwamnan jahar Kano shawarar samarmusu da sabbin kayan aiki na zamani wadanda zasu taimaka sosai wajen shirin kota kwana akowanne lokaci.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started