
Daga Abubakar Sale Yakub
Jami’an Kamfanin na MTN suka bayyana hakan a loakcin da suka karbi tawagar Babban Maitaimakawa Gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf, kan sha’anin Kasuwar Kantin Kwari, SA Ibrahim Company, a ranar Laraba.
Sun ce kamfanin Yana aiki cikin sa’o’i 24 domin kyautatuwa abokan Huldarsa.
Da yake jawabi Alhaji Ibrahim Garba Kamfani (SA Kantin Kwari) yace su kawo ziyarar kamfanin sadarwa na MTN wato (MOBILE TELEPHONE NETWORK MTN) don tattaunawa da jami’an kamfanin gameda matsalar network da yan Kasuwar Kantin Kwari suke fama da ita lokaci zuwa lokaci.
“Babban makasudin wannan ziyara shine samarda hanyar bunkasa karfin network din don jindadi da walwar yan kasuwa, inji S.A Kantin Kwari.
Bayan tattaunawa da Jami’an Kamfanin MTN da ke Jihar Kano daga karshe kamfanin yayi alkawarin shiga cikin kasuwar don bunkasa karfin network din da kuma kawar da matsalar gaba daya.
Leave a comment