Gwamnatin Kano ta nemi hadin kan Hukumar Kiyaye afkuwar hadura ta kasa domin kyautatuwar kasuwanci a Kasuwar Kantin Kwari -SA Kamfani

Gwamnatin Jihar Kano ta nemi hadin Hukumar Kiyaye afkuwar hadura da ta kasa road Safety wajen samar da kyakykyawan Yana in kasuwanci a Kasuwar Kantin Kwari.
Maitaimakawa Gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf, kan sha’anin Kasuwar Kantin Kwari, Hon. Ibrahim Garba Kamfani, ya buakci hadin akan a lokacin da ya Kai ziyarar bangirma da kulla Alaka a Shelkwatar Hukumar ta FRSC a birnin Kano.

Yace ziyarar zata taimaka wajen kulla Alaka da sanin dokoki daka’idoji da  ya kamata direbobin Kasuwar Kantin Kwari su bi a loakcin Jami’an Road Safety suke aiki.

Hon Ibrahim Kamfani, ya yabawa Hukumar kan yadda take gudanar da ayyukanta, Yana Mai cewa Babban dalilin ziyarar shine samar da fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu.

Da yake nasa jawabin Babban Kwamandan Hukumar Kiyaye afkuwar hadura ta kasa reshen Jihar Kano, yace a shirye Hukumar take tayi aiki tare da ofishin SA. Ibrahim Kamfani.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started