Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano ya jinjinawa Sanata Kawu Sumaila kan kudirin kafa Kwalejin Gwamnatin Tarayya a garin Karaye-Barista Dederi

Daga_ Abubakar Sale Yakub

Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Haruna Dederi ya jinjinawa Sanata Kawu Sumaila, mai wakilatar Kano ta Kudu bisa kudirin da ya gabatar a zauren Majalisar Dattijai na neman kafa Babbar Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Musamman a Karamar Hukumar Karaye a ranar  Laraba a birnin Abuja.

Barista Dederi, ya bayyana hakane a birnin Kano a lokacin da yake zantawa da manema Labarai a yau Laraba.

Yace wannnan kudirin anyi masa karatun farko a yau ya kuma yi masa fatan cigaba da gwagwarmaya wajen ganin samar da kwalejin ya tabbata.

Ya cigaba da cewa a lokacin da yake Majalisa ta 9, yayi kokarin gabatar da kudirin har ya kai ga karatu na biyu har na anyi zaman sauraren ra’ayin Jama’a.

Barista Haruna Dederi, yace dukkan Al’ummr Jihar Kano da kasa Najeriya zasu amfana da Kwalejin da zarar an kafata.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started