HAJJ 2024-Maniyatan aikin hajji na Jihar Kano zasu fara ajiye naira miliyan 4.5

DG Pilgrims Kano

Daga Abubakar Sale Yakub

Hukumar jin da din alhazai ta Jihar Kano a hukumance ta kaddamar da shirye shiryen aikin Hajji na shekarar 2024 a ranar Alhamis.
Babban Daraktan Hukumar Alh Laminu Rabi’u, ya bayyana hakan a loakcin da yake kaddamar da Shirin a taron manema Labarai a ofishinsa a birnin Kano.

Yace Hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON  ta baiwa Jihar Kano kujeru dubu 5 da Dari 9 da 34.

A cewarsa , bisa umarnin Hukumar Kaso 60 n adadin kujerun na maniyatan jihane da suka fito daga Kano kaso 49 suna tsarin Adashin gata dake karkashin Bankin Ja’iz.

Babban Daraktan, ya sanar da cewa ko wane maniyaci zai ajiye naira miliyan 4.5 domin aikin Hajjin Badi, ya kara da cewa wannnan baya cikin masu tsarin Adashin gata na Hajj Serving Scheme.

Lamiru Rabi’u , yace sun kaddamar da shirye shiryen aikin Hajjin badi a yau Alhamis, Yana Mai cewa sun kammala raba kujerun ga kananan hukumomin Jihar Kano 44″.

“Mun Kuma umarci Jami’an Alhazai a matakin kananan hukumomi dasu fara karbar kudaden ajiya” acewar Laminu Rabi’u

Babban Daraktan, ya kuma cewa Hukumar jin dadin alhazan ta shirya  kaucewa dukkan wani kalubale da aka fuskanta a hajjin bara .

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started