Gwamnatin Kano ta musanta wani rahoton Facebook da ke cewa mutane 10 sun rasu rana daya a Asibitin Koyawar na Nasarawa.

Dr . Mansur Nagoda

Daga Abubakar Sale Yakub

Hukumar kula da Asibitoci ta Jihar Kano ta musanta rahoton dake yawo a kafar sada zumunta cewa marassa lafiya 10 sun rasu a Rana daya a Asibitin Koyawar na Abdullahi Wase.

Babban Sakataren Hukumar kula da Asibitoci ta Jihar Kano Dr Mansur Nagoda ya mayar da martani kan labarin da wani Mai suna Hussaini Ahmad ya wallafa a shafinsa na Facebook.
A cikin binciken da Ma’aikatar Lafiya da  Hukumar kula da Asibitoci suka  gudanar sun ce daga 1 ga watan Oktoba zuwa 10, babu wani rahoto   da ke nuna cewa mutane 10 sun rasu a rana daya.
Binciken yace marassa lafiya 15 suka rasu a ranaku daban daban.
A nata bangaren Shugabar Asibitin Dr. Hadiza Sa’id, ta bayyana cewa marassa lafiya 2 daga bangaren kula da mata suka rasu, a bangaren kula Maza marar lafiya 1, ne ya rasu a sashin fida, sai kuma Maza uku marassa lafiya daga bangare. Medical Ward, mutane bakwai marassa lafiya 7 suka rasu daga sashin kulawa ta musamman( ICU)  sai Kuma mutane biyu daga bangaren Amenity.

Babban Sakataren Hukumar, Dr Mansur Nagoda yace an sake tura Ma’aikatan lafiya 10 da likitoci uku zuwa sashin bayar da agajin gaggawa  domin inganta aikin da ake a wajen.
Dr. Nagoda, yace sun himmatu wajen cika alkawarin da Gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf ya dauka  na sake inganta tsarin kula da lafiya da samar da kayan aiki.
Ya Kuma nuna damuwa sabo da yadda wasu mutane suke kokarin yiwa ayyukan Gwamnatin Kano zagon kasa, domin su Sanya Tsaro a zukatan Jama’a suki zuwa karbar magunguna a Asibitocin Jihar Kano.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started