
Daga- Abubakar Sale Yakub
An saki Jami’in alhazai na Karamar Hukumar Bebeji Alh Sagir Umar Kofa, wanda akai garkuwa da shi a kwanakin baya.
Darakta Janar Hukumar jin da din alhazai ta Jihar Kano, Alh Laminu Rabi’u Danpappa, ya ziyarci Jami’in ya kuma jajanta masa tare da addu’ar Allah ya kiyaye afkuwar hakan a nan gaba.
Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su Kara kaimi wajen ganin sun kubutar da sauran mutanen da suka rage wajen bata garin.
Da yake jawabi Jami’in Alhazan Alh Sagir Umar Kofa, an samu nasarar kubutar dashi a karamar Hukumar Ikara a Jihar Kaduna bayan da ya kwashe tsahon kwanaki 38 a wajen masu garkuwar.
Alh Sagir Kofa yace masu garkuwar sun dira a kauyen Galadimawa da ke kan hanyar Zaria Ina suka karbi naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa Yan uwa mutanen da suna kama..
Ya Kuma ya bawa Darakta Janar bisa kokarinsa tare da kulawa a garesshi.
Jami’in Alhazan na Karamar Hukumar Bebeji yayi Addu’ar kiyaye al’ummar Jihar Kano daga faruwar irin wannnan iftila’i.
Leave a comment