Ma’aikatar raya karkara ta gudanar da yashe magudanan ruwa a unguwar Rjiyar Lemo da sauran gurare.

Daga NBA

Kwamishinan ma’aikatar raya karkara da cigaban al’umma Alh. Hamza Safiyanu Kachako tare da ma’aikatan ma’aikatar sun shiga aikin yashe magudanun ruwa a Unguwar Rijiyar Lemo da sauran wuraren da aka gudanar da aikin anan birnin kano.

Kwamishinan wanda ya yi gargadi akan masu zubar da shara a magudanun ruwa ya bukaci al’umma su rika shirya irin wannan aikin gayya domin kare afkuwar ambaliyar ruwa da zaizayar kasa a yankunansu.

A nasu jawaban babban sakatare Alh. Musa Yahaya Bichi da babban mai taimakawa gwamna na musamman akan harkokin ma’aikatar Alh. Rilwanu Umar Kanwa sun yaba da kokarin kungiyoyin aikin gayya bisa Shirya aikin yashe magudanun ruwan.

Shugaban kwamitin koli da kungiyoyin aikin gayya na jahar kano Alh. Bashar Nasidi wanda ya yabawa kwamishinan bisa ba su kayan aikin gayya ya kuma ba da tabbacin cigaba da jajircewa wajen gudanar da wannan aiki a sassan jahar kano tare da ba da gudummawa a aiyukan ma’aikatar.

Kwamishinan ya duba aikin yashe magudanun ruwan a wurare daban daban dake nan birnin kano.

COV/NBA

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started