Bukatar Samar da Cibiyar Tattara bukatun Al’ummar Kano-Dr. Gali Sa’idu, BUK.

Daga NBA

Shugaban Tsangayar Ilimin Manyan da Aiyukan Al’umma ta Jami’ar Bayero dake nan kano Dr. Gali Sa’idu ya bayyana muhimmancin gwamnati ta samar da cibiyar tattara bayanai akan bukatun al’ummar jahar kano domin binsu daki daki wajen kokarin magance su.

Dr. Gali Sa’idu ya bayyana haka ne a yayin kammala horar da ma’aikatan ma’aikatar Raya karkara da cigaban al’umma wadda aka gudanar a Cibiyar Nazarin jinsin Dan Adam dake sabuwar Jami’ar Bayero.

Shugaban Tsangayar ya nuna gamsuwarsa bisa yanda mahalarta bitar suka nuna kwazo tare da fahimtar bitar yanda yakamata.

An nasa jawabin Kwamishinan ma’aikatar raya karkara da cigaban al’umma Alh. Hamza Safiyanu Kachako ya ja hankalin ma’aikatan ma’aikatar da su kara himma da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu domin samun sakamako mai kyau.

Da yake mika takardun shaidar kammala samun horon ga ma’aikatan Alh. Hamza Safiyanu Kachako ya bukace su da su yi kyakkyawan amfani da wannan horon domin ci gaban ma’aikatar da ma jihar kano baki daya.

Mahalarta taron sun ba da tabbacin yin amfani da ilimin da aka koya a yayin bitar.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started