
Daga Abubakar Sale Yakub
Kungiyar tsofaffin daliban Makarantar Sakandiren Lautai da ke garin Gumel a Jihar Jigawa sun karrama Darakta Janaral na hukumar Jin dadin alhazai ta jihar Kano Alh.Laminu Rabiu a ranar Laraba Ofishinsa.
Da yake jawabi tun da farko shugaban kungiyar na kasa Alh. Nafiu Shuaibu, ya bayyana kyawawan halayen Laminu Rabiu wadanda suka Hadar da gaskiya, rikon Amana, kawaici da kuma aiki tukuri ,Wanda sakamakon haka ne aka bashi shugaban Bayar da abinci wato ( Kitchen Prefect )
A karshe Babban Darakta Janaral yayi godiya a madadin hukumar Jin dadin alhazai ta jihar Kano abisa wannan karramawa da akayi masa.
Leave a comment