
Daga NBA_IOF
Gwamnatin jahar kano za ta samar da wadataccen kayan aiki ga kungiyoyin aikin gayya domin yashe magudanun Ruwa.
Kwamishinan ma’aikatar raya karkara da cigaban al’umma Alh. Hamza Safiyanu Kachako ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kwamitin koli na aikin gayya a ofishinsa dake ma’aikatar.
Alh. Hamza Safiyanu Kachako wanda ya bayyana muhimmancin kwamitin ga al’umma ya ce samar da kayan aikin zai karawa kungiyoyin karfin guiwa domin cigaba da jajircewa wajen yashe magudanun Ruwa akai akai.
A nasa jawabin shugaban kwamitin Comrade Aminu Garba Kofar Na’isa ya ce sun ziyarci kwamishinan ne domin taya shi murnar nada shi a matsayin sabon kwamishinan ma’aikatar tare da jaddada kudirin kwamitin na goyon bayan manufofin gwamnati na tallafawa al’umma.
Kazalika, kwamishinan ma’aikatar raya karkara da cigaban al’umma Alh. Hamza Safiyanu Kachako ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar cigaban matasan garin Kachako KAYDA bisa jagorancin Comrade Rabi’u Sale Damina da Mustafa Aliyu Kachako.
Shugabannin sun ce ziyarci kwamishinan ne domin taya shi murna da ba shi shawarwari da kuma yin addu’o’i alkhairi domin samun nasara a nauyin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya dora masa na jagorancin ma’aikatar.
Leave a comment