
Daga_NBA
Sabon Ko’odinatan cibiyar koyar da sana’o’i ta Aliko Dangote dake Tamburawa anan kano Alh. Alkasim Hussaini Wudil ya yi alkawarin bunkasa aiyukan cibiyar domin amfanin al’umar jahar kano da arewacin kasar nan.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya shiga ofishinsa domin kama aiki a ranar Larabar nan.
Alh. Alkasim Hussaini Wudil, ya ce zai hada guiwa da masu ruwa da tsaki da hukumomi da ma’aikatun gwamnati da kuma kungiyoyi masu zaman kansu domin horar da dubban matasa da mata sana’o’in dogaro da kai domin dogaro da kansu domin inganta tattalin arzikin jahar kano da Kasa baki daya.
A yayin da yake ganawa da ma’aikatan cibiyar Alh. Alkashim Hussaini Wudil ya kuma yi alwashin inganta walwalar ma’aikatan cibiyar sannan ya gargade su akan su guji fashi ko makara zuwa wajen aiki.
A nasa bangaren babban jami’in dake kula da aiyukan cibiyar Alh. Halilu Garba, ya ce akwai sassa 20 da kwasa kwasai 13 da ake koyar da sana’o’i daban daban a cibiyar.
Alh. Halilu Garba, wanda bayyana matsalolin da cibiyar ke fusknta ya kuma ba da tabbacin hadin kai da goyon bayan dukkanin ma’aikatan cibiyar domin cimma nasarar da aka sa a gaba.
Leave a comment