
Daga NAJ
Gwamnatin jihar Kano ta gano manyan matsalolin makabartu a cikin birnin Kano.
Shugaban kwamitin kuma kwamishinan ma’aikatar raya karkara da bunkasa rayuwar al’umma Alh. Hamza Safiyanu Kachako, ya bayyana haka ne jim kadan bayan karbar rahoto akan halin da suke ciki daga ‘yan kwamitin duba Makabartun a ofishinsa.
Ya ce rahoton ya nuna Makabartun ba su wadataciyar katanga da ta kewaye su, da rashin magudanun Ruwa da fitulu da rijiyoyin bursa Tse da kuma rashib masu gadi da kayan aikinsu.
Alh.Hamza Safiyanu Kachako, ya kara da cewa ma’aikatar za ta mika rahoton ga gwamna Abba Kabir domin amincewar sa.
Daga nan sai ya ba da tabbacin gwamnatin jihar kano wajen inganta yanayin makabartu.
Kwamishinan ya gargadi mutane da su guji zubar da shara a makabartu.
Daga cikin wuraren da kwamitin ya ziyarta akwai makabartar Gama da ta Unguwa Uku da ta Tarauni da kuma ta titin kotu.
Sauran sun hada da makabartar Gandun Albasa da ta Dan Agundi da ta Hauren Shanu dake karamar hukumar Gwale.
Leave a comment