Sabon Gwamnan Jihar Osun ya dakatar da Sarakuna uku a Jihar

Sabon gwamnan jihar Osun Sanata Ademola Adeleke ya bayar da umarnin dakatar da sarakunan gargajiya uku da tsohon gwamnan jihar Gboyega Oyetola ya naɗa kwana guda bayan kama aiki.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Olawale Rasheed ya fitar ranar Litinin ya ce gwamnan ya ɗauki matakin ne domin a cewarsa ba a bi ƙa’idar da ta dace ba wajen naɗin sarakunan

Haka kuma gwamnan ya bayar da umarnin sake duba dokar naɗin sarakunan gargajiya a jihar.

A ranar Lahadi ne dai aka rantsar da Sanata Ademola Adeleke a matsayin sabon gwamnan jihar Osun.

Yayin wani jawabi da ya gabatar bayan rantsuwar kama aikin, Mista Adeleke ya ce zai gyara abin da ya kira ”rashin adalci” da cin hanci ko wasu tsare-tsare da gwamnatocin da suka gabata suka aikata wa al’umar jihar.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started