
Shugaban Majalisar limaman Juma’a na jahar Kano Sheik MUHAMMAD Nasir Adam ya nemi Limamai su yi addu’o’i a ranar Juma’a me zuwa don samun zaman lafiya a lokutan gudanar campaign da zabuka dake tafe.
Ya yi kiranne a lokacin da ya ke zantawa da wakilin mu Abubakar Sale Yakub, a birnin Kano ya bukaci ‘Yan siyasa dasu kaucewa yin amfani da matasa domin haifar da rikici, Shehin Malamin ya ja hankalin iyaye dasu lura da Kai komon ya yansu.
Sheik Muhammad Nasir Adam, ya cigaba da yin kira ga Limaman Jihar Kano, dasu kaucewa yin huduba akan duk kan wani lamari da basu da hakikanin iliminsa.
ASY
Leave a comment