Gwamnatin Kano ta kashe naira biliyan 2, wajen sayo motocin Bas bas guda 100 dan inganta sufuri a cikin birni.

Gwamnan Kano Ganduje ya kaddamar da motocin sufurin da zasuyi aiki a cikin birnin Kano, motocin akwai Bas bas guda 100 da Tasi guda 50, yana mai cewa zasu fara jigilar fasinjoji daga Jogana da Yan kura zuwa Janguza.

Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da motocin Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Ganduje, yace aikin gina hanyoyi da Gadojin sama da fadada titunan dake Kano da sauran ayyuka la’akari da cewa Kano ciniyar kasuwanci ce da masana’antu.

Ganduje, ya Kara da cewa motocin Kanawa manyan Bas bas guda dari daya, zasu dauki mutane masu yawa a lokaci guda, an kuma Sayo su akan kudi naira miliyan dubu biyu.

Da yake jawabi tun da gari Shugaban Kwamitin Shirin Rabi’u Bichi, Wanda ya gabatar da motocin Bas bas din , ya jinjinawa aniyar Gwamnan Kano, ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki dasu bunkasa shirin zuwa mataki nagaba.

Yace kananan hukumomin cikin birnin guda takwas za a rika ganin gilmawar motocin, ya kuma masu zuba jari dasu shiga adama dasu a cikin sabon tsarin sufurin.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started