Shugaban Amurika Joe Biden, ya fitar da wani umarnin shugaban ƙasa inda ya yi afuwa ga duk Amurkawan da kotunan tarayya suka samu da laifi, saboda “kawai an kama su da tabar wiwi”.

Rahotanni sun ce matakin zai shafi akasari mutane ƙalilan ne na hukuncin da ke da alaƙa da tabar wiwi saboda mafi yawa a kotunan jihohi ake ƙarar su.
Kaɗan ya rage sanarwar Shugaba Biden ta halasta tu’ammali da wiwi, kamar yadda ya yi alƙawari lokacin da yake yaƙin neman zaɓe.
Ƙuri’un jin ra’ayoyi na baya-bayan nan sun nuna cewa mafi yawan Amurkawa sun yi imani cewa kamata ya yi a halasta sha da dillancin tabar wiwi.
“Aika mutane zuwa gidan yari saboda suna ɗauke da wiwi ya birkita rayuwar mutane fiye da adadi kuma a tsare mutane saboda halayyar da jihohi da dama a yanzu ba sa hanawa,” in ji sanarwar Joe Biden ta ranar Alhamis.
Leave a comment