


Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya kai ziyarar duba aikin ginin katafariyar gadar nan mai hawa uku.
wadda aka sakawa sunan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wadda ke Hotoro, NNPC Roundabout.
Ana dab da kammala aikin gadar mai hawa uku wacce akewa laqabi da “karshen zance”.
Da zarar an kammala za ta saukake yanayin chunkoson da ake fama dashi a wannan shataletalen.
hakan zai kara bunkasa harkokin kasuwanci kasancewarta babbar hanyar da mutane daga makwabtan jihohi ke shigowa Jihar Kano domin harkokin kasuwancin su.

Leave a comment