HOTUNAN GIDAN DA AKA HADE YANKIN KUDANCI DA AREWACIN NAJERIYA

Gidan Amalgamation shi ne gidan zama na gwamnati a lokacin mulkin mallaka.

Gidan yana a karamar hukumar Ikot Abasi a jihar Akwa Ibom.

Wani tsohon gida mai bangon bulo dake cikin wani fili da ke kewaye da bishiyoyi.

Gidan Amalgamation wuri ne na tarihi, Shine Gidan haihuwar Najeriya.

Ginin da Lord Lugard ya rattaba hannu a kan dokar ne ya haifar da hadewar yankin Arewa da Kudancin Najeriya a shekarar 1914,

Ta haka ne aka samar da wata Al’umma guda daya da aka fi sani da Najeriya ta yau.

Har ila yau, ginin ne Janar Olusegun Obasanjo (tsohon kwamandan sojojin Najeriya) da Janar Phillip Effiong na sojojin Biafra suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta kawo karshen yakin basasar Najeriya a watan Janairun 1970.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started