Kar ku yadda ku zabi masu kashe mutane

Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya gargaɗi ƴan Najeriya da kada su kuskura su zaɓi masu kashe mutane a babban zaɓe dake tafe.

Jonathan ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a garin Uyo na Jihar Akwa Ibom a taron addu’o’i da aka yi kan cikar jihar ta Akwa Ibom shekara 35 da samun jiha.

Yana mai cewa mutanen da za su ɗauki wuƙaƙe da bindigogi da duk sauran makamai su je su kashe mutane saboda siyasa maƙiyan al’umma ne.

Haka kuma Mista Jonathan ɗin ya yaba wa Gwamnan Udom Emmanuel na jihar kan ayyukan ci gaba da ya kai jihar.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started