Dan Kasar China ya yiwa wata bahaushiya kisan gilla a Kano

Nazifi Dukawa

Ummukulsum Sani da ake zargin Dan Kasar China ta halakata

Ana dai zargin  Geng Quanrong, da kashe wata budurwa Mai suna Ummukulsum Sani ta hanyar caccaka mata wuka.

Wasu shedun gani da Ido Kuma dake kusa da inda lamarin ya faru sun bayyana yadda suka ganewa idonsu wannnan mummunan lamari a unguwar Janbulo a cikin birnin Kano.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar SP. Abdullahi Haruna Kiyawa  a santarwa da manema Labarai a Kano yace  ce  Dan Kasar Chinan Mai shekaru 47 ya haura  gidan su Ummukulsum  ya halakata.

Dan Kasar  Chinan dai yana zargin Ummukulsum da yaudararsa, ta hanyar kin aurensa bayan ya dade yana yi mata hidima.

Hakan ce ta sanya ransa ya baciya kuma ya je har gidansu dake unguwar Jan bullo  Yamadawa a Dorayi Babba ya haura cikin gidan don aiwatar da mugun nufinsa.

Bayan ya haura ne ya shiga dakin yarinyar ta taga, ya zaro wuka ya fara caccaka mata a wuya da kafufunta.

SP  Kiyawa, yace “mun  samu Labarin kuma kwamishinan ‘yan sanda na Jihar  Kano ya tura jami’ansa karkashin DPOn Dorayi Babba CP Abubakar Lawan”.

Ya cigaba  da cewa da isarsu ne suka dauki yarinyar zuwa Asibitin Kwararru na  Murtala  Muhammad likitoci suka   tabbatar da cewa tabrasu.

Kiyawa, ya ce tuni suka kama  mutumin da ake  zargi tare da kaishi  shalkwatar Yan sanda dake Bompai domin ci gaba da bincike.

Bayan ya soka mata wukar ne kuma mahaifyarta ta yi ihun a kawo taimako inda wami matashi ya yi kukan kura ya Kai dauki.

ya rawaito cewa kakakin rundunar yansandan jihar sp abdullahi haruna
Kiyawa yace da samun Labarin ne kuma kwamishinan yan sandan ya tura jami’ansa karkashin DPO  Dorayi Babba CP Abubakar Lawan.

Anasa Jawabin shugaban gamaiyarr kungiyoyin Kare hakkin Dan Adam ta kasa da kasa kwamarat haruna ayagi ya bayyana cewa zasu bibiyi wanna Batu domin Ganin an Yankee masa hukunci dai dai da abinda ya aikita

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started