Mutane hudu da suka aikata fyade kotu tayi musu daurin Rai da rai

Wata babbar kotu mai lamba 6 da ke birnin Kudu a jihar Jigawa ta yanke wa wasu mutum hudu da ta samu da laifin aikata fyade, hukuncin daurin rai-da-rai.

Sanarwar da Ma’aikatar Shari’a ta jihar ta fitar ranar Laraba, mai dauke da sa hannun jami’ar hulda ta ma’aikatar, Zainab Baba Santali, ta ce mutanen sun aikata babban laifi, duba da sashi na 283 na kundin dokar jihar na 2012 da aka sabunta.

Mutanen sun hada da Umar Danladi da Abdussalam Sale da Auwalu Yunusa da kuma Mu’azu Abdurrahman.

Da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Musa Ubale, ya ce an samu Umar Danladi da laifin yi wa wata yarinya mai shekara takwas fyade bayan tursasata lokacin da take komawa gida daga makaranta.

Mai Shari’a Ubale, ya kara da cewa mutum na biyu da aka yanke wa hukunci mai suna Abdussalam Sale, ana zarginsa ne da yi wa wata mai shekara 12 fyade.

Ya hadu da yarinyar ne a kauyen Kishin Gishin Gawa, inda ya yaudare ta ta hanyar aiken ta ta saya masa wani abu, bayan dawowarta ya kamata da karfi ya yi mata fyade.

Sai dai, ya musanta aikata laifin bayan kama shi da aka yi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, shi kuma Auwalu Yunusa da ya fito daga garin Kafin Fulani, an zarge shi da yi wa wata yarinya mai shekara shida fyade bayan da ya yi mata barazanar cewa zai kashe ta muddin ta fada wa wani.

Kwanaki bayan faruwar lamarin, yarinyar ta kasa tafiya, inda nan ne ta kira sunan Yunusa a matsayin wanda ya yi mata fyade.

Mai Shari’a Musa Ubale, ya ce mutum na hudu da aka yanke wa hukunci, Mu’azu Abdulrahman daga Sabuwar Gwaram, an same shi da laifin tare wata yarinya mai shekara takwas lokacin da take komawa gida daga makaranta, inda ya kai ta zuwa wani gona da kuma yi mata fyade.

Sai dai, bayan gabatar da shi a gaban kotu, ya musanta aikata laifin, inda a nasa bangaren, lauya mai yanke hukunci, ya kira shaidu uku domin gabatar da su suka bayar da shaida.

Tambarin kotu

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started