Mataimakin Gwamnan jihar Kano APC Dr. Nasiru Yusuf Gawuna (Khadimul Dawa’atul Islamiyya) ya karɓi Tsohon Mai Neman Zama Ɗan Takarar Majalisar jiha Na Ƙaramar Hukumar Gabasawa Malam Bashir Sa’ad Zakirai (Limamin Masallacin Juma’a a garin Zakirai) tare da jama’ar sa.
Mutane sun ajiye tafiyar jam’iyyar NNPP inda suka dawo jamiyyar APC, ƙarƙashin jagorancin Ɗan Takarar Majalisar Tarayya Na Ƙananan Hukumomin Gazawa da Gabasawa Hon. Mahmoud Muhammad Santsi.
Yayin karɓar mutane da suka sauya Sheƙar an gudanar da bikin a dakin taro na Ofishin Mataimakin Gwamna dake fadar Gwamnatin jihar Kano.
Cikin wadanda suka halarci taron akwai Manyan Mataimaka Na Musamman ga Gwamna Kan Fannoni daban-daban dake Ofishin Mataimakin Gwamna da kuma Shugaban Jam’iyyar APC Na Gabasawa Alh. Aminu Manga Zakirai.

Leave a comment